نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2946 | 26 | 14 | ولهم علي ذنب فأخاف أن يقتلون |
| | | "Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni." |
|
2947 | 26 | 15 | قال كلا فاذهبا بآياتنا إنا معكم مستمعون |
| | | Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre." |
|
2948 | 26 | 16 | فأتيا فرعون فقولا إنا رسول رب العالمين |
| | | "Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne." |
|
2949 | 26 | 17 | أن أرسل معنا بني إسرائيل |
| | | "Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu." |
|
2950 | 26 | 18 | قال ألم نربك فينا وليدا ولبثت فينا من عمرك سنين |
| | | Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?" |
|
2951 | 26 | 19 | وفعلت فعلتك التي فعلت وأنت من الكافرين |
| | | "Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?" |
|
2952 | 26 | 20 | قال فعلتها إذا وأنا من الضالين |
| | | Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi." |
|
2953 | 26 | 21 | ففررت منكم لما خفتكم فوهب لي ربي حكما وجعلني من المرسلين |
| | | "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni." |
|
2954 | 26 | 22 | وتلك نعمة تمنها علي أن عبدت بني إسرائيل |
| | | "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla." |
|
2955 | 26 | 23 | قال فرعون وما رب العالمين |
| | | Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?" |
|