نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2933 | 26 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم طسم |
| | | ¦. S̃. M̃. |
|
2934 | 26 | 2 | تلك آيات الكتاب المبين |
| | | Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne. |
|
2935 | 26 | 3 | لعلك باخع نفسك ألا يكونوا مؤمنين |
| | | Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba! |
|
2936 | 26 | 4 | إن نشأ ننزل عليهم من السماء آية فظلت أعناقهم لها خاضعين |
| | | Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai. |
|
2937 | 26 | 5 | وما يأتيهم من ذكر من الرحمن محدث إلا كانوا عنه معرضين |
| | | Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa. |
|
2938 | 26 | 6 | فقد كذبوا فسيأتيهم أنباء ما كانوا به يستهزئون |
| | | To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu. |
|
2939 | 26 | 7 | أولم يروا إلى الأرض كم أنبتنا فيها من كل زوج كريم |
| | | Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau? |
|
2940 | 26 | 8 | إن في ذلك لآية وما كان أكثرهم مؤمنين |
| | | Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba. |
|
2941 | 26 | 9 | وإن ربك لهو العزيز الرحيم |
| | | Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama. |
|
2942 | 26 | 10 | وإذ نادى ربك موسى أن ائت القوم الظالمين |
| | | Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai. |
|