نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2920 | 25 | 65 | والذين يقولون ربنا اصرف عنا عذاب جهنم إن عذابها كان غراما |
| | | Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra |
|
2921 | 25 | 66 | إنها ساءت مستقرا ومقاما |
| | | "Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni." |
|
2922 | 25 | 67 | والذين إذا أنفقوا لم يسرفوا ولم يقتروا وكان بين ذلك قواما |
| | | Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa. |
|
2923 | 25 | 68 | والذين لا يدعون مع الله إلها آخر ولا يقتلون النفس التي حرم الله إلا بالحق ولا يزنون ومن يفعل ذلك يلق أثاما |
| | | Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka, |
|
2924 | 25 | 69 | يضاعف له العذاب يوم القيامة ويخلد فيه مهانا |
| | | A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce. |
|
2925 | 25 | 70 | إلا من تاب وآمن وعمل عملا صالحا فأولئك يبدل الله سيئاتهم حسنات وكان الله غفورا رحيما |
| | | Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai. |
|
2926 | 25 | 71 | ومن تاب وعمل صالحا فإنه يتوب إلى الله متابا |
| | | Kuma wanda ya tũba, kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah. |
|
2927 | 25 | 72 | والذين لا يشهدون الزور وإذا مروا باللغو مروا كراما |
| | | Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci. |
|
2928 | 25 | 73 | والذين إذا ذكروا بآيات ربهم لم يخروا عليها صما وعميانا |
| | | Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame da makãfi. |
|
2929 | 25 | 74 | والذين يقولون ربنا هب لنا من أزواجنا وذرياتنا قرة أعين واجعلنا للمتقين إماما |
| | | Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya mu shũgabanni ga mãsu taƙawa." |
|