نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2915 | 25 | 60 | وإذا قيل لهم اسجدوا للرحمن قالوا وما الرحمن أنسجد لما تأمرنا وزادهم نفورا |
| | | Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana ta ƙãra musu gudu. |
|
2916 | 25 | 61 | تبارك الذي جعل في السماء بروجا وجعل فيها سراجا وقمرا منيرا |
| | | Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta. |
|
2917 | 25 | 62 | وهو الذي جعل الليل والنهار خلفة لمن أراد أن يذكر أو أراد شكورا |
| | | Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde. |
|
2918 | 25 | 63 | وعباد الرحمن الذين يمشون على الأرض هونا وإذا خاطبهم الجاهلون قالوا سلاما |
| | | Kuma bãyin Mai rahama su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya). |
|
2919 | 25 | 64 | والذين يبيتون لربهم سجدا وقياما |
| | | Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu. |
|
2920 | 25 | 65 | والذين يقولون ربنا اصرف عنا عذاب جهنم إن عذابها كان غراما |
| | | Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra |
|
2921 | 25 | 66 | إنها ساءت مستقرا ومقاما |
| | | "Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni." |
|
2922 | 25 | 67 | والذين إذا أنفقوا لم يسرفوا ولم يقتروا وكان بين ذلك قواما |
| | | Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa. |
|
2923 | 25 | 68 | والذين لا يدعون مع الله إلها آخر ولا يقتلون النفس التي حرم الله إلا بالحق ولا يزنون ومن يفعل ذلك يلق أثاما |
| | | Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka, |
|
2924 | 25 | 69 | يضاعف له العذاب يوم القيامة ويخلد فيه مهانا |
| | | A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce. |
|