نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2796 | 24 | 5 | إلا الذين تابوا من بعد ذلك وأصلحوا فإن الله غفور رحيم |
| | | Fãce waɗanda suka tũbadaga bãyan wannan, kuma suka gyãru, to lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
|
2797 | 24 | 6 | والذين يرمون أزواجهم ولم يكن لهم شهداء إلا أنفسهم فشهادة أحدهم أربع شهادات بالله إنه لمن الصادقين |
| | | Kuma waɗanda ke jĩfar mãtan aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga magasganta.' |
|
2798 | 24 | 7 | والخامسة أن لعنت الله عليه إن كان من الكاذبين |
| | | Kuma ta biyar cẽwa 'La'anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga maƙaryata.' |
|
2799 | 24 | 8 | ويدرأ عنها العذاب أن تشهد أربع شهادات بالله إنه لمن الكاذبين |
| | | Kuma yanã tunkuɗe mata azãba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah, 'Lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga maƙaryata.' |
|
2800 | 24 | 9 | والخامسة أن غضب الله عليها إن كان من الصادقين |
| | | Kuma tã biyar cẽwa 'Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga magasganta.' |
|
2801 | 24 | 10 | ولولا فضل الله عليكم ورحمته وأن الله تواب حكيم |
| | | Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku, da rahamarSa, kuma cẽwa Allah Mai karɓar tũba ne, Mai hikima! |
|
2802 | 24 | 11 | إن الذين جاءوا بالإفك عصبة منكم لا تحسبوه شرا لكم بل هو خير لكم لكل امرئ منهم ما اكتسب من الإثم والذي تولى كبره منهم له عذاب عظيم |
| | | Lalle ne waɗanda suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma. |
|
2803 | 24 | 12 | لولا إذ سمعتموه ظن المؤمنون والمؤمنات بأنفسهم خيرا وقالوا هذا إفك مبين |
| | | Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?" |
|
2804 | 24 | 13 | لولا جاءوا عليه بأربعة شهداء فإذ لم يأتوا بالشهداء فأولئك عند الله هم الكاذبون |
| | | Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata. |
|
2805 | 24 | 14 | ولولا فضل الله عليكم ورحمته في الدنيا والآخرة لمسكم في ما أفضتم فيه عذاب عظيم |
| | | Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne, dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa. |
|