نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2758 | 23 | 85 | سيقولون لله قل أفلا تذكرون |
| | | Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?" |
|
2759 | 23 | 86 | قل من رب السماوات السبع ورب العرش العظيم |
| | | Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?" |
|
2760 | 23 | 87 | سيقولون لله قل أفلا تتقون |
| | | Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?" |
|
2761 | 23 | 88 | قل من بيده ملكوت كل شيء وهو يجير ولا يجار عليه إن كنتم تعلمون |
| | | Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?" |
|
2762 | 23 | 89 | سيقولون لله قل فأنى تسحرون |
| | | Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku?" |
|
2763 | 23 | 90 | بل أتيناهم بالحق وإنهم لكاذبون |
| | | Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne. |
|
2764 | 23 | 91 | ما اتخذ الله من ولد وما كان معه من إله إذا لذهب كل إله بما خلق ولعلا بعضهم على بعض سبحان الله عما يصفون |
| | | Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa. |
|
2765 | 23 | 92 | عالم الغيب والشهادة فتعالى عما يشركون |
| | | Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka. |
|
2766 | 23 | 93 | قل رب إما تريني ما يوعدون |
| | | Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi." |
|
2767 | 23 | 94 | رب فلا تجعلني في القوم الظالمين |
| | | "Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai." |
|