نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2720 | 23 | 47 | فقالوا أنؤمن لبشرين مثلنا وقومهما لنا عابدون |
| | | Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne." |
|
2721 | 23 | 48 | فكذبوهما فكانوا من المهلكين |
| | | Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku. |
|
2722 | 23 | 49 | ولقد آتينا موسى الكتاب لعلهم يهتدون |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu. |
|
2723 | 23 | 50 | وجعلنا ابن مريم وأمه آية وآويناهما إلى ربوة ذات قرار ومعين |
| | | Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari. |
|
2724 | 23 | 51 | يا أيها الرسل كلوا من الطيبات واعملوا صالحا إني بما تعملون عليم |
| | | Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne. |
|
2725 | 23 | 52 | وإن هذه أمتكم أمة واحدة وأنا ربكم فاتقون |
| | | Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa. |
|
2726 | 23 | 53 | فتقطعوا أمرهم بينهم زبرا كل حزب بما لديهم فرحون |
| | | Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su. |
|
2727 | 23 | 54 | فذرهم في غمرتهم حتى حين |
| | | To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci. |
|
2728 | 23 | 55 | أيحسبون أنما نمدهم به من مال وبنين |
| | | Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya, |
|
2729 | 23 | 56 | نسارع لهم في الخيرات بل لا يشعرون |
| | | Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri? |
|