نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2679 | 23 | 6 | إلا على أزواجهم أو ما ملكت أيمانهم فإنهم غير ملومين |
| | | Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne. |
|
2680 | 23 | 7 | فمن ابتغى وراء ذلك فأولئك هم العادون |
| | | Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi. |
|
2681 | 23 | 8 | والذين هم لأماناتهم وعهدهم راعون |
| | | Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne. |
|
2682 | 23 | 9 | والذين هم على صلواتهم يحافظون |
| | | Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa. |
|
2683 | 23 | 10 | أولئك هم الوارثون |
| | | Waɗannan, sũ ne magãda. |
|
2684 | 23 | 11 | الذين يرثون الفردوس هم فيها خالدون |
| | | Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne. |
|
2685 | 23 | 12 | ولقد خلقنا الإنسان من سلالة من طين |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka. |
|
2686 | 23 | 13 | ثم جعلناه نطفة في قرار مكين |
| | | Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya. |
|
2687 | 23 | 14 | ثم خلقنا النطفة علقة فخلقنا العلقة مضغة فخلقنا المضغة عظاما فكسونا العظام لحما ثم أنشأناه خلقا آخر فتبارك الله أحسن الخالقين |
| | | Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa. |
|
2688 | 23 | 15 | ثم إنكم بعد ذلك لميتون |
| | | Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne. |
|