نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2670 | 22 | 75 | الله يصطفي من الملائكة رسلا ومن الناس إن الله سميع بصير |
| | | Allah nã zãɓen Manzanni daga malã'iku kuma daga mutãne. Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani. |
|
2671 | 22 | 76 | يعلم ما بين أيديهم وما خلفهم وإلى الله ترجع الأمور |
| | | Yanã sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura. |
|
2672 | 22 | 77 | يا أيها الذين آمنوا اركعوا واسجدوا واعبدوا ربكم وافعلوا الخير لعلكم تفلحون |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammãninku, ku sami babban rabo. |
|
2673 | 22 | 78 | وجاهدوا في الله حق جهاده هو اجتباكم وما جعل عليكم في الدين من حرج ملة أبيكم إبراهيم هو سماكم المسلمين من قبل وفي هذا ليكون الرسول شهيدا عليكم وتكونوا شهداء على الناس فأقيموا الصلاة وآتوا الزكاة واعتصموا بالله هو مولاكم فنعم المولى ونعم النصير |
| | | Kuma ku yi jihãdi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan (Littãfi ya yi muku sũna Musulmi), dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako. |
|
2674 | 23 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم قد أفلح المؤمنون |
| | | Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ. |
|
2675 | 23 | 2 | الذين هم في صلاتهم خاشعون |
| | | Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne. |
|
2676 | 23 | 3 | والذين هم عن اللغو معرضون |
| | | Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne. |
|
2677 | 23 | 4 | والذين هم للزكاة فاعلون |
| | | Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne. |
|
2678 | 23 | 5 | والذين هم لفروجهم حافظون |
| | | Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne. |
|
2679 | 23 | 6 | إلا على أزواجهم أو ما ملكت أيمانهم فإنهم غير ملومين |
| | | Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne. |
|