نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2640 | 22 | 45 | فكأين من قرية أهلكناها وهي ظالمة فهي خاوية على عروشها وبئر معطلة وقصر مشيد |
| | | Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka. |
|
2641 | 22 | 46 | أفلم يسيروا في الأرض فتكون لهم قلوب يعقلون بها أو آذان يسمعون بها فإنها لا تعمى الأبصار ولكن تعمى القلوب التي في الصدور |
| | | Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta. |
|
2642 | 22 | 47 | ويستعجلونك بالعذاب ولن يخلف الله وعده وإن يوما عند ربك كألف سنة مما تعدون |
| | | Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa. |
|
2643 | 22 | 48 | وكأين من قرية أمليت لها وهي ظالمة ثم أخذتها وإلي المصير |
| | | Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azãba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kãma ta, kuma zuwa gare Ni makõma take. |
|
2644 | 22 | 49 | قل يا أيها الناس إنما أنا لكم نذير مبين |
| | | Ka ce: "Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa." |
|
2645 | 22 | 50 | فالذين آمنوا وعملوا الصالحات لهم مغفرة ورزق كريم |
| | | To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci. |
|
2646 | 22 | 51 | والذين سعوا في آياتنا معاجزين أولئك أصحاب الجحيم |
| | | Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne. |
|
2647 | 22 | 52 | وما أرسلنا من قبلك من رسول ولا نبي إلا إذا تمنى ألقى الشيطان في أمنيته فينسخ الله ما يلقي الشيطان ثم يحكم الله آياته والله عليم حكيم |
| | | Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri, sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima. |
|
2648 | 22 | 53 | ليجعل ما يلقي الشيطان فتنة للذين في قلوبهم مرض والقاسية قلوبهم وإن الظالمين لفي شقاق بعيد |
| | | Dõmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfãwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukãtansu akwai cũta, da mãsu ƙẽƙasassun zukãtansu. Kuma lalle ne azzãlumai haƙĩƙa, sunã a cikin sãɓãnimai nĩsa. |
|
2649 | 22 | 54 | وليعلم الذين أوتوا العلم أنه الحق من ربك فيؤمنوا به فتخبت له قلوبهم وإن الله لهاد الذين آمنوا إلى صراط مستقيم |
| | | Kuma dõmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dõmin su yi ĩmãni da shi sabõda zukãtansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmãni ne zuwa ga hanya madaidaiciya. |
|