نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2598 | 22 | 3 | ومن الناس من يجادل في الله بغير علم ويتبع كل شيطان مريد |
| | | Akwai daga mutãne wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai. |
|
2599 | 22 | 4 | كتب عليه أنه من تولاه فأنه يضله ويهديه إلى عذاب السعير |
| | | An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr. |
|
2600 | 22 | 5 | يا أيها الناس إن كنتم في ريب من البعث فإنا خلقناكم من تراب ثم من نطفة ثم من علقة ثم من مضغة مخلقة وغير مخلقة لنبين لكم ونقر في الأرحام ما نشاء إلى أجل مسمى ثم نخرجكم طفلا ثم لتبلغوا أشدكم ومنكم من يتوفى ومنكم من يرد إلى أرذل العمر لكيلا يعلم من بعد علم شيئا وترى الأرض هامدة فإذا أنزلنا عليها الماء اهتزت وربت وأنبتت من كل زوج بهيج |
| | | Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin ¡iyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa. |
|
2601 | 22 | 6 | ذلك بأن الله هو الحق وأنه يحيي الموتى وأنه على كل شيء قدير |
| | | Wancan ne dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kõme. |
|
2602 | 22 | 7 | وأن الساعة آتية لا ريب فيها وأن الله يبعث من في القبور |
| | | Kuma lalle ne Sa'ar Tãshin ¡iyãma mai zuwa ce, bãbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yanã tãyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura. |
|
2603 | 22 | 8 | ومن الناس من يجادل في الله بغير علم ولا هدى ولا كتاب منير |
| | | Kuma daga mutãne akwai mai yin musu ga Allah bã da wani ilmi ba kuma bã da wata shiriya ba, kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba. |
|
2604 | 22 | 9 | ثاني عطفه ليضل عن سبيل الله له في الدنيا خزي ونذيقه يوم القيامة عذاب الحريق |
| | | Yanã mai karkatar da sãshensa dõmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yanã da wani wulãkanci a dũniya, kuma Munã ɗanɗana masa azãbar gõbara a Rãnar ¡iyãma. |
|
2605 | 22 | 10 | ذلك بما قدمت يداك وأن الله ليس بظلام للعبيد |
| | | (A ce masa): "Wancan azaba sabõda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zãlunci ga bãyinSa ba." |
|
2606 | 22 | 11 | ومن الناس من يعبد الله على حرف فإن أصابه خير اطمأن به وإن أصابته فتنة انقلب على وجهه خسر الدنيا والآخرة ذلك هو الخسران المبين |
| | | Kuma daga mutãne akwai mai bauta wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya sãme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta sãme shi, sai ya jũya bãya a kan fuskarsa. Yã yi hasãrar dũniya da Lãhira. Waccan ita ce hasãra bayyananna. |
|
2607 | 22 | 12 | يدعو من دون الله ما لا يضره وما لا ينفعه ذلك هو الضلال البعيد |
| | | Yanã kiran baicin Allah, abin da bã ya cũtarsa da abin da bã ya amfãninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa. |
|