نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2533 | 21 | 50 | وهذا ذكر مبارك أنزلناه أفأنتم له منكرون |
| | | Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi? |
|
2534 | 21 | 51 | ولقد آتينا إبراهيم رشده من قبل وكنا به عالمين |
| | | Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi. |
|
2535 | 21 | 52 | إذ قال لأبيه وقومه ما هذه التماثيل التي أنتم لها عاكفون |
| | | Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?" |
|
2536 | 21 | 53 | قالوا وجدنا آباءنا لها عابدين |
| | | Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu." |
|
2537 | 21 | 54 | قال لقد كنتم أنتم وآباؤكم في ضلال مبين |
| | | Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna." |
|
2538 | 21 | 55 | قالوا أجئتنا بالحق أم أنت من اللاعبين |
| | | Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne?" |
|
2539 | 21 | 56 | قال بل ربكم رب السماوات والأرض الذي فطرهن وأنا على ذلكم من الشاهدين |
| | | Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka." |
|
2540 | 21 | 57 | وتالله لأكيدن أصنامكم بعد أن تولوا مدبرين |
| | | "Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya." |
|
2541 | 21 | 58 | فجعلهم جذاذا إلا كبيرا لهم لعلهم إليه يرجعون |
| | | Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi. |
|
2542 | 21 | 59 | قالوا من فعل هذا بآلهتنا إنه لمن الظالمين |
| | | Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai." |
|