نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2516 | 21 | 33 | وهو الذي خلق الليل والنهار والشمس والقمر كل في فلك يسبحون |
| | | Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu a cikin wani sarari suKe iyo. |
|
2517 | 21 | 34 | وما جعلنا لبشر من قبلك الخلد أفإن مت فهم الخالدون |
| | | Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama? |
|
2518 | 21 | 35 | كل نفس ذائقة الموت ونبلوكم بالشر والخير فتنة وإلينا ترجعون |
| | | Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku. |
|
2519 | 21 | 36 | وإذا رآك الذين كفروا إن يتخذونك إلا هزوا أهذا الذي يذكر آلهتكم وهم بذكر الرحمن هم كافرون |
| | | Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta ne. |
|
2520 | 21 | 37 | خلق الإنسان من عجل سأريكم آياتي فلا تستعجلون |
| | | An halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nẽmiyin gaggãwa. |
|
2521 | 21 | 38 | ويقولون متى هذا الوعد إن كنتم صادقين |
| | | Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya?" |
|
2522 | 21 | 39 | لو يعلم الذين كفروا حين لا يكفون عن وجوههم النار ولا عن ظهورهم ولا هم ينصرون |
| | | Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba. |
|
2523 | 21 | 40 | بل تأتيهم بغتة فتبهتهم فلا يستطيعون ردها ولا هم ينظرون |
| | | Ã'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba. |
|
2524 | 21 | 41 | ولقد استهزئ برسل من قبلك فحاق بالذين سخروا منهم ما كانوا به يستهزئون |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su. |
|
2525 | 21 | 42 | قل من يكلؤكم بالليل والنهار من الرحمن بل هم عن ذكر ربهم معرضون |
| | | Ka ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu. |
|