نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2493 | 21 | 10 | لقد أنزلنا إليكم كتابا فيه ذكركم أفلا تعقلون |
| | | Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta? |
|
2494 | 21 | 11 | وكم قصمنا من قرية كانت ظالمة وأنشأنا بعدها قوما آخرين |
| | | Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta. |
|
2495 | 21 | 12 | فلما أحسوا بأسنا إذا هم منها يركضون |
| | | Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta. |
|
2496 | 21 | 13 | لا تركضوا وارجعوا إلى ما أترفتم فيه ومساكنكم لعلكم تسألون |
| | | "Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku." |
|
2497 | 21 | 14 | قالوا يا ويلنا إنا كنا ظالمين |
| | | Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci." |
|
2498 | 21 | 15 | فما زالت تلك دعواهم حتى جعلناهم حصيدا خامدين |
| | | Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu. |
|
2499 | 21 | 16 | وما خلقنا السماء والأرض وما بينهما لاعبين |
| | | Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba. |
|
2500 | 21 | 17 | لو أردنا أن نتخذ لهوا لاتخذناه من لدنا إن كنا فاعلين |
| | | Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa. |
|
2501 | 21 | 18 | بل نقذف بالحق على الباطل فيدمغه فإذا هو زاهق ولكم الويل مما تصفون |
| | | Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa. |
|
2502 | 21 | 19 | وله من في السماوات والأرض ومن عنده لا يستكبرون عن عبادته ولا يستحسرون |
| | | Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurinSa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya. |
|