نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2486 | 21 | 3 | لاهية قلوبهم وأسروا النجوى الذين ظلموا هل هذا إلا بشر مثلكم أفتأتون السحر وأنتم تبصرون |
| | | Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?" |
|
2487 | 21 | 4 | قال ربي يعلم القول في السماء والأرض وهو السميع العليم |
| | | Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani." |
|
2488 | 21 | 5 | بل قالوا أضغاث أحلام بل افتراه بل هو شاعر فليأتنا بآية كما أرسل الأولون |
| | | Ã'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko." |
|
2489 | 21 | 6 | ما آمنت قبلهم من قرية أهلكناها أفهم يؤمنون |
| | | Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni? |
|
2490 | 21 | 7 | وما أرسلنا قبلك إلا رجالا نوحي إليهم فاسألوا أهل الذكر إن كنتم لا تعلمون |
| | | Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato idan kun kasance ba ku sani ba. |
|
2491 | 21 | 8 | وما جعلناهم جسدا لا يأكلون الطعام وما كانوا خالدين |
| | | Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba. |
|
2492 | 21 | 9 | ثم صدقناهم الوعد فأنجيناهم ومن نشاء وأهلكنا المسرفين |
| | | Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa. |
|
2493 | 21 | 10 | لقد أنزلنا إليكم كتابا فيه ذكركم أفلا تعقلون |
| | | Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta? |
|
2494 | 21 | 11 | وكم قصمنا من قرية كانت ظالمة وأنشأنا بعدها قوما آخرين |
| | | Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta. |
|
2495 | 21 | 12 | فلما أحسوا بأسنا إذا هم منها يركضون |
| | | Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta. |
|