نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2466 | 20 | 118 | إن لك ألا تجوع فيها ولا تعرى |
| | | Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba. |
|
2467 | 20 | 119 | وأنك لا تظمأ فيها ولا تضحى |
| | | "Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba." |
|
2468 | 20 | 120 | فوسوس إليه الشيطان قال يا آدم هل أدلك على شجرة الخلد وملك لا يبلى |
| | | Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa?" |
|
2469 | 20 | 121 | فأكلا منها فبدت لهما سوآتهما وطفقا يخصفان عليهما من ورق الجنة وعصى آدم ربه فغوى |
| | | Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace. |
|
2470 | 20 | 122 | ثم اجتباه ربه فتاب عليه وهدى |
| | | Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi). |
|
2471 | 20 | 123 | قال اهبطا منها جميعا بعضكم لبعض عدو فإما يأتينكم مني هدى فمن اتبع هداي فلا يضل ولا يشقى |
| | | Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala." |
|
2472 | 20 | 124 | ومن أعرض عن ذكري فإن له معيشة ضنكا ونحشره يوم القيامة أعمى |
| | | "Kuma wanda ya bijire daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho." |
|
2473 | 20 | 125 | قال رب لم حشرتني أعمى وقد كنت بصيرا |
| | | Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani?" |
|
2474 | 20 | 126 | قال كذلك أتتك آياتنا فنسيتها وكذلك اليوم تنسى |
| | | Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyinMu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka." |
|
2475 | 20 | 127 | وكذلك نجزي من أسرف ولم يؤمن بآيات ربه ولعذاب الآخرة أشد وأبقى |
| | | Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita, kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa |
|