نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2452 | 20 | 104 | نحن أعلم بما يقولون إذ يقول أمثلهم طريقة إن لبثتم إلا يوما |
| | | Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda." |
|
2453 | 20 | 105 | ويسألونك عن الجبال فقل ينسفها ربي نسفا |
| | | Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa, |
|
2454 | 20 | 106 | فيذرها قاعا صفصفا |
| | | Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi. |
|
2455 | 20 | 107 | لا ترى فيها عوجا ولا أمتا |
| | | "Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu." |
|
2456 | 20 | 108 | يومئذ يتبعون الداعي لا عوج له وخشعت الأصوات للرحمن فلا تسمع إلا همسا |
| | | A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya. |
|
2457 | 20 | 109 | يومئذ لا تنفع الشفاعة إلا من أذن له الرحمن ورضي له قولا |
| | | A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da magan |
|
2458 | 20 | 110 | يعلم ما بين أيديهم وما خلفهم ولا يحيطون به علما |
| | | Yanã sanin abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani. |
|
2459 | 20 | 111 | وعنت الوجوه للحي القيوم وقد خاب من حمل ظلما |
| | | Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe. |
|
2460 | 20 | 112 | ومن يعمل من الصالحات وهو مؤمن فلا يخاف ظلما ولا هضما |
| | | Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa. |
|
2461 | 20 | 113 | وكذلك أنزلناه قرآنا عربيا وصرفنا فيه من الوعيد لعلهم يتقون أو يحدث لهم ذكرا |
| | | Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa. |
|