نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2446 | 20 | 98 | إنما إلهكم الله الذي لا إله إلا هو وسع كل شيء علما |
| | | Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci dukkan kõme da ilmi. |
|
2447 | 20 | 99 | كذلك نقص عليك من أنباء ما قد سبق وقد آتيناك من لدنا ذكرا |
| | | Kamar wancan ne Muke lãbartãwa a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu. |
|
2448 | 20 | 100 | من أعرض عنه فإنه يحمل يوم القيامة وزرا |
| | | Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma. |
|
2449 | 20 | 101 | خالدين فيه وساء لهم يوم القيامة حملا |
| | | Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma. |
|
2450 | 20 | 102 | يوم ينفخ في الصور ونحشر المجرمين يومئذ زرقا |
| | | A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu. |
|
2451 | 20 | 103 | يتخافتون بينهم إن لبثتم إلا عشرا |
| | | Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma." |
|
2452 | 20 | 104 | نحن أعلم بما يقولون إذ يقول أمثلهم طريقة إن لبثتم إلا يوما |
| | | Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda." |
|
2453 | 20 | 105 | ويسألونك عن الجبال فقل ينسفها ربي نسفا |
| | | Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa, |
|
2454 | 20 | 106 | فيذرها قاعا صفصفا |
| | | Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi. |
|
2455 | 20 | 107 | لا ترى فيها عوجا ولا أمتا |
| | | "Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu." |
|