نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2432 | 20 | 84 | قال هم أولاء على أثري وعجلت إليك رب لترضى |
| | | Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda." |
|
2433 | 20 | 85 | قال فإنا قد فتنا قومك من بعدك وأضلهم السامري |
| | | Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su." |
|
2434 | 20 | 86 | فرجع موسى إلى قومه غضبان أسفا قال يا قوم ألم يعدكم ربكم وعدا حسنا أفطال عليكم العهد أم أردتم أن يحل عليكم غضب من ربكم فأخلفتم موعدي |
| | | Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?" |
|
2435 | 20 | 87 | قالوا ما أخلفنا موعدك بملكنا ولكنا حملنا أوزارا من زينة القوم فقذفناها فكذلك ألقى السامري |
| | | Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa." |
|
2436 | 20 | 88 | فأخرج لهم عجلا جسدا له خوار فقالوا هذا إلهكم وإله موسى فنسي |
| | | "Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta." |
|
2437 | 20 | 89 | أفلا يرون ألا يرجع إليهم قولا ولا يملك لهم ضرا ولا نفعا |
| | | Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni? |
|
2438 | 20 | 90 | ولقد قال لهم هارون من قبل يا قوم إنما فتنتم به وإن ربكم الرحمن فاتبعوني وأطيعوا أمري |
| | | Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna." |
|
2439 | 20 | 91 | قالوا لن نبرح عليه عاكفين حتى يرجع إلينا موسى |
| | | Suka ce: "Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta, sai Mũsã ya kõmo zuwa gare mu." |
|
2440 | 20 | 92 | قال يا هارون ما منعك إذ رأيتهم ضلوا |
| | | (Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace." |
|
2441 | 20 | 93 | ألا تتبعن أفعصيت أمري |
| | | "Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?" |
|