نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2383 | 20 | 35 | إنك كنت بنا بصيرا |
| | | "Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu." |
|
2384 | 20 | 36 | قال قد أوتيت سؤلك يا موسى |
| | | Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!" |
|
2385 | 20 | 37 | ولقد مننا عليك مرة أخرى |
| | | "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam." |
|
2386 | 20 | 38 | إذ أوحينا إلى أمك ما يوحى |
| | | "A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka." |
|
2387 | 20 | 39 | أن اقذفيه في التابوت فاقذفيه في اليم فليلقه اليم بالساحل يأخذه عدو لي وعدو له وألقيت عليك محبة مني ولتصنع على عيني |
| | | "Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan ganiNa." |
|
2388 | 20 | 40 | إذ تمشي أختك فتقول هل أدلكم على من يكفله فرجعناك إلى أمك كي تقر عينها ولا تحزن وقتلت نفسا فنجيناك من الغم وفتناك فتونا فلبثت سنين في أهل مدين ثم جئت على قدر يا موسى |
| | | "A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã! |
|
2389 | 20 | 41 | واصطنعتك لنفسي |
| | | "Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina." |
|
2390 | 20 | 42 | اذهب أنت وأخوك بآياتي ولا تنيا في ذكري |
| | | "Ka tafi kai da ɗan'uwanka game da ãyõyiNa, kuma kada ku yi rauni ga ambatõNa." |
|
2391 | 20 | 43 | اذهبا إلى فرعون إنه طغى |
| | | "Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)." |
|
2392 | 20 | 44 | فقولا له قولا لينا لعله يتذكر أو يخشى |
| | | "Sai ku gaya masa magana mai laushi, tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro." |
|