نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2363 | 20 | 15 | إن الساعة آتية أكاد أخفيها لتجزى كل نفس بما تسعى |
| | | "Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa." |
|
2364 | 20 | 16 | فلا يصدنك عنها من لا يؤمن بها واتبع هواه فتردى |
| | | "Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka." |
|
2365 | 20 | 17 | وما تلك بيمينك يا موسى |
| | | "Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!" |
|
2366 | 20 | 18 | قال هي عصاي أتوكأ عليها وأهش بها على غنمي ولي فيها مآرب أخرى |
| | | Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci na dabam a gare ta." |
|
2367 | 20 | 19 | قال ألقها يا موسى |
| | | Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!" |
|
2368 | 20 | 20 | فألقاها فإذا هي حية تسعى |
| | | Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa. |
|
2369 | 20 | 21 | قال خذها ولا تخف سنعيدها سيرتها الأولى |
| | | Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko." |
|
2370 | 20 | 22 | واضمم يدك إلى جناحك تخرج بيضاء من غير سوء آية أخرى |
| | | "Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam." |
|
2371 | 20 | 23 | لنريك من آياتنا الكبرى |
| | | "Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya." |
|
2372 | 20 | 24 | اذهب إلى فرعون إنه طغى |
| | | "Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)." |
|