نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2352 | 20 | 4 | تنزيلا ممن خلق الأرض والسماوات العلى |
| | | (An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka. |
|
2353 | 20 | 5 | الرحمن على العرش استوى |
| | | Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi. |
|
2354 | 20 | 6 | له ما في السماوات وما في الأرض وما بينهما وما تحت الثرى |
| | | Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya. |
|
2355 | 20 | 7 | وإن تجهر بالقول فإنه يعلم السر وأخفى |
| | | Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa. |
|
2356 | 20 | 8 | الله لا إله إلا هو له الأسماء الحسنى |
| | | Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau. |
|
2357 | 20 | 9 | وهل أتاك حديث موسى |
| | | Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka? |
|
2358 | 20 | 10 | إذ رأى نارا فقال لأهله امكثوا إني آنست نارا لعلي آتيكم منها بقبس أو أجد على النار هدى |
| | | A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar." |
|
2359 | 20 | 11 | فلما أتاها نودي يا موسى |
| | | Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!" |
|
2360 | 20 | 12 | إني أنا ربك فاخلع نعليك إنك بالواد المقدس طوى |
| | | "Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa." |
|
2361 | 20 | 13 | وأنا اخترتك فاستمع لما يوحى |
| | | "Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi." |
|