نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
236 | 2 | 229 | الطلاق مرتان فإمساك بمعروف أو تسريح بإحسان ولا يحل لكم أن تأخذوا مما آتيتموهن شيئا إلا أن يخافا ألا يقيما حدود الله فإن خفتم ألا يقيما حدود الله فلا جناح عليهما فيما افتدت به تلك حدود الله فلا تعتدوها ومن يتعد حدود الله فأولئك هم الظالمون |
| | | Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai. |
|
237 | 2 | 230 | فإن طلقها فلا تحل له من بعد حتى تنكح زوجا غيره فإن طلقها فلا جناح عليهما أن يتراجعا إن ظنا أن يقيما حدود الله وتلك حدود الله يبينها لقوم يعلمون |
| | | Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani. |
|
238 | 2 | 231 | وإذا طلقتم النساء فبلغن أجلهن فأمسكوهن بمعروف أو سرحوهن بمعروف ولا تمسكوهن ضرارا لتعتدوا ومن يفعل ذلك فقد ظلم نفسه ولا تتخذوا آيات الله هزوا واذكروا نعمت الله عليكم وما أنزل عليكم من الكتاب والحكمة يعظكم به واتقوا الله واعلموا أن الله بكل شيء عليم |
| | | Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne. |
|
239 | 2 | 232 | وإذا طلقتم النساء فبلغن أجلهن فلا تعضلوهن أن ينكحن أزواجهن إذا تراضوا بينهم بالمعروف ذلك يوعظ به من كان منكم يؤمن بالله واليوم الآخر ذلكم أزكى لكم وأطهر والله يعلم وأنتم لا تعلمون |
| | | Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba. |
|
240 | 2 | 233 | والوالدات يرضعن أولادهن حولين كاملين لمن أراد أن يتم الرضاعة وعلى المولود له رزقهن وكسوتهن بالمعروف لا تكلف نفس إلا وسعها لا تضار والدة بولدها ولا مولود له بولده وعلى الوارث مثل ذلك فإن أرادا فصالا عن تراض منهما وتشاور فلا جناح عليهما وإن أردتم أن تسترضعوا أولادكم فلا جناح عليكم إذا سلمتم ما آتيتم بالمعروف واتقوا الله واعلموا أن الله بما تعملون بصير |
| | | Kuma mãsu haifuwa (sakakku) suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne. |
|
241 | 2 | 234 | والذين يتوفون منكم ويذرون أزواجا يتربصن بأنفسهن أربعة أشهر وعشرا فإذا بلغن أجلهن فلا جناح عليكم فيما فعلن في أنفسهن بالمعروف والله بما تعملون خبير |
| | | Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne. |
|
242 | 2 | 235 | ولا جناح عليكم فيما عرضتم به من خطبة النساء أو أكننتم في أنفسكم علم الله أنكم ستذكرونهن ولكن لا تواعدوهن سرا إلا أن تقولوا قولا معروفا ولا تعزموا عقدة النكاح حتى يبلغ الكتاب أجله واعلموا أن الله يعلم ما في أنفسكم فاحذروه واعلموا أن الله غفور حليم |
| | | Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri. |
|
243 | 2 | 236 | لا جناح عليكم إن طلقتم النساء ما لم تمسوهن أو تفرضوا لهن فريضة ومتعوهن على الموسع قدره وعلى المقتر قدره متاعا بالمعروف حقا على المحسنين |
| | | Kuma bãbu laifi a kanku idan kun saki mãtã matuƙar ba ku shãfe su ba, kuma ba ku yanka musu sadãki ba. Kuma ku bã su kyautar dãɗaɗãwa, a kan mawadãci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; dõmin dãɗaɗrwa, da alhẽri, wãjibi ne a kan mãsu kyautatãwa. |
|
244 | 2 | 237 | وإن طلقتموهن من قبل أن تمسوهن وقد فرضتم لهن فريضة فنصف ما فرضتم إلا أن يعفون أو يعفو الذي بيده عقدة النكاح وأن تعفوا أقرب للتقوى ولا تنسوا الفضل بينكم إن الله بما تعملون بصير |
| | | Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne. |
|
245 | 2 | 238 | حافظوا على الصلوات والصلاة الوسطى وقوموا لله قانتين |
| | | Ku tsare lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah. |
|