نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2348 | 19 | 98 | وكم أهلكنا قبلهم من قرن هل تحس منهم من أحد أو تسمع لهم ركزا |
| | | Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu? |
|
2349 | 20 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم طه |
| | | ¦.H. |
|
2350 | 20 | 2 | ما أنزلنا عليك القرآن لتشقى |
| | | Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba. |
|
2351 | 20 | 3 | إلا تذكرة لمن يخشى |
| | | Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah. |
|
2352 | 20 | 4 | تنزيلا ممن خلق الأرض والسماوات العلى |
| | | (An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka. |
|
2353 | 20 | 5 | الرحمن على العرش استوى |
| | | Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi. |
|
2354 | 20 | 6 | له ما في السماوات وما في الأرض وما بينهما وما تحت الثرى |
| | | Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya. |
|
2355 | 20 | 7 | وإن تجهر بالقول فإنه يعلم السر وأخفى |
| | | Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa. |
|
2356 | 20 | 8 | الله لا إله إلا هو له الأسماء الحسنى |
| | | Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau. |
|
2357 | 20 | 9 | وهل أتاك حديث موسى |
| | | Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka? |
|