نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2343 | 19 | 93 | إن كل من في السماوات والأرض إلا آتي الرحمن عبدا |
| | | Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã. |
|
2344 | 19 | 94 | لقد أحصاهم وعدهم عدا |
| | | Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya. |
|
2345 | 19 | 95 | وكلهم آتيه يوم القيامة فردا |
| | | Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai. |
|
2346 | 19 | 96 | إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات سيجعل لهم الرحمن ودا |
| | | Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so. |
|
2347 | 19 | 97 | فإنما يسرناه بلسانك لتبشر به المتقين وتنذر به قوما لدا |
| | | Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma. |
|
2348 | 19 | 98 | وكم أهلكنا قبلهم من قرن هل تحس منهم من أحد أو تسمع لهم ركزا |
| | | Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu? |
|
2349 | 20 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم طه |
| | | ¦.H. |
|
2350 | 20 | 2 | ما أنزلنا عليك القرآن لتشقى |
| | | Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba. |
|
2351 | 20 | 3 | إلا تذكرة لمن يخشى |
| | | Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah. |
|
2352 | 20 | 4 | تنزيلا ممن خلق الأرض والسماوات العلى |
| | | (An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka. |
|