نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2332 | 19 | 82 | كلا سيكفرون بعبادتهم ويكونون عليهم ضدا |
| | | Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu. |
|
2333 | 19 | 83 | ألم تر أنا أرسلنا الشياطين على الكافرين تؤزهم أزا |
| | | Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa? |
|
2334 | 19 | 84 | فلا تعجل عليهم إنما نعد لهم عدا |
| | | Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa. |
|
2335 | 19 | 85 | يوم نحشر المتقين إلى الرحمن وفدا |
| | | A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma. |
|
2336 | 19 | 86 | ونسوق المجرمين إلى جهنم وردا |
| | | Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa. |
|
2337 | 19 | 87 | لا يملكون الشفاعة إلا من اتخذ عند الرحمن عهدا |
| | | Ba su mal1akar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama. |
|
2338 | 19 | 88 | وقالوا اتخذ الرحمن ولدا |
| | | Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!" |
|
2339 | 19 | 89 | لقد جئتم شيئا إدا |
| | | Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni. |
|
2340 | 19 | 90 | تكاد السماوات يتفطرن منه وتنشق الأرض وتخر الجبال هدا |
| | | Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu. |
|
2341 | 19 | 91 | أن دعوا للرحمن ولدا |
| | | Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama. |
|