نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2273 | 19 | 23 | فأجاءها المخاض إلى جذع النخلة قالت يا ليتني مت قبل هذا وكنت نسيا منسيا |
| | | Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!" |
|
2274 | 19 | 24 | فناداها من تحتها ألا تحزني قد جعل ربك تحتك سريا |
| | | Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki. |
|
2275 | 19 | 25 | وهزي إليك بجذع النخلة تساقط عليك رطبا جنيا |
| | | "Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu." |
|
2276 | 19 | 26 | فكلي واشربي وقري عينا فإما ترين من البشر أحدا فقولي إني نذرت للرحمن صوما فلن أكلم اليوم إنسيا |
| | | "Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba." |
|
2277 | 19 | 27 | فأتت به قومها تحمله قالوا يا مريم لقد جئت شيئا فريا |
| | | Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma! |
|
2278 | 19 | 28 | يا أخت هارون ما كان أبوك امرأ سوء وما كانت أمك بغيا |
| | | "Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba." |
|
2279 | 19 | 29 | فأشارت إليه قالوا كيف نكلم من كان في المهد صبيا |
| | | Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?" |
|
2280 | 19 | 30 | قال إني عبد الله آتاني الكتاب وجعلني نبيا |
| | | Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi." |
|
2281 | 19 | 31 | وجعلني مباركا أين ما كنت وأوصاني بالصلاة والزكاة ما دمت حيا |
| | | "Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai." |
|
2282 | 19 | 32 | وبرا بوالدتي ولم يجعلني جبارا شقيا |
| | | "Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri." |
|