نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2260 | 19 | 10 | قال رب اجعل لي آية قال آيتك ألا تكلم الناس ثلاث ليال سويا |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai." |
|
2261 | 19 | 11 | فخرج على قومه من المحراب فأوحى إليهم أن سبحوا بكرة وعشيا |
| | | Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma." |
|
2262 | 19 | 12 | يا يحيى خذ الكتاب بقوة وآتيناه الحكم صبيا |
| | | Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro. |
|
2263 | 19 | 13 | وحنانا من لدنا وزكاة وكان تقيا |
| | | Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa. |
|
2264 | 19 | 14 | وبرا بوالديه ولم يكن جبارا عصيا |
| | | Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba. |
|
2265 | 19 | 15 | وسلام عليه يوم ولد ويوم يموت ويوم يبعث حيا |
| | | Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai. |
|
2266 | 19 | 16 | واذكر في الكتاب مريم إذ انتبذت من أهلها مكانا شرقيا |
| | | Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas. |
|
2267 | 19 | 17 | فاتخذت من دونهم حجابا فأرسلنا إليها روحنا فتمثل لها بشرا سويا |
| | | Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci. |
|
2268 | 19 | 18 | قالت إني أعوذ بالرحمن منك إن كنت تقيا |
| | | Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!" |
|
2269 | 19 | 19 | قال إنما أنا رسول ربك لأهب لك غلاما زكيا |
| | | Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki." |
|