نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2255 | 19 | 5 | وإني خفت الموالي من ورائي وكانت امرأتي عاقرا فهب لي من لدنك وليا |
| | | "Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa." |
|
2256 | 19 | 6 | يرثني ويرث من آل يعقوب واجعله رب رضيا |
| | | "Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!" |
|
2257 | 19 | 7 | يا زكريا إنا نبشرك بغلام اسمه يحيى لم نجعل له من قبل سميا |
| | | (Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni." |
|
2258 | 19 | 8 | قال رب أنى يكون لي غلام وكانت امرأتي عاقرا وقد بلغت من الكبر عتيا |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?" |
|
2259 | 19 | 9 | قال كذلك قال ربك هو علي هين وقد خلقتك من قبل ولم تك شيئا |
| | | Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba." |
|
2260 | 19 | 10 | قال رب اجعل لي آية قال آيتك ألا تكلم الناس ثلاث ليال سويا |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai." |
|
2261 | 19 | 11 | فخرج على قومه من المحراب فأوحى إليهم أن سبحوا بكرة وعشيا |
| | | Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma." |
|
2262 | 19 | 12 | يا يحيى خذ الكتاب بقوة وآتيناه الحكم صبيا |
| | | Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro. |
|
2263 | 19 | 13 | وحنانا من لدنا وزكاة وكان تقيا |
| | | Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa. |
|
2264 | 19 | 14 | وبرا بوالديه ولم يكن جبارا عصيا |
| | | Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba. |
|