نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2232 | 18 | 92 | ثم أتبع سببا |
| | | Sa'an nan kuma ya bi hanya. |
|
2233 | 18 | 93 | حتى إذا بلغ بين السدين وجد من دونهما قوما لا يكادون يفقهون قولا |
| | | Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba. |
|
2234 | 18 | 94 | قالوا يا ذا القرنين إن يأجوج ومأجوج مفسدون في الأرض فهل نجعل لك خرجا على أن تجعل بيننا وبينهم سدا |
| | | Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?" |
|
2235 | 18 | 95 | قال ما مكني فيه ربي خير فأعينوني بقوة أجعل بينكم وبينهم ردما |
| | | Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu." |
|
2236 | 18 | 96 | آتوني زبر الحديد حتى إذا ساوى بين الصدفين قال انفخوا حتى إذا جعله نارا قال آتوني أفرغ عليه قطرا |
| | | "Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa." |
|
2237 | 18 | 97 | فما اسطاعوا أن يظهروه وما استطاعوا له نقبا |
| | | Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujẽwa gare shi ba. |
|
2238 | 18 | 98 | قال هذا رحمة من ربي فإذا جاء وعد ربي جعله دكاء وكان وعد ربي حقا |
| | | Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce." |
|
2239 | 18 | 99 | وتركنا بعضهم يومئذ يموج في بعض ونفخ في الصور فجمعناهم جمعا |
| | | Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa. |
|
2240 | 18 | 100 | وعرضنا جهنم يومئذ للكافرين عرضا |
| | | Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa. |
|
2241 | 18 | 101 | الذين كانت أعينهم في غطاء عن ذكري وكانوا لا يستطيعون سمعا |
| | | Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa. |
|