نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2212 | 18 | 72 | قال ألم أقل إنك لن تستطيع معي صبرا |
| | | Ya ce: "Ashe ban ce, lalle kai, bã za ka iya yin haƙuri tãre da ni ba?" |
|
2213 | 18 | 73 | قال لا تؤاخذني بما نسيت ولا ترهقني من أمري عسرا |
| | | Ya ce: "Kada ka kãma ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarĩna." |
|
2214 | 18 | 74 | فانطلقا حتى إذا لقيا غلاما فقتله قال أقتلت نفسا زكية بغير نفس لقد جئت شيئا نكرا |
| | | Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma." |
|
2215 | 18 | 75 | قال ألم أقل لك إنك لن تستطيع معي صبرا |
| | | Ya ce: "Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ ba?" |
|
2216 | 18 | 76 | قال إن سألتك عن شيء بعدها فلا تصاحبني قد بلغت من لدني عذرا |
| | | Ya ce: "Idan na tambaye ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni." |
|
2217 | 18 | 77 | فانطلقا حتى إذا أتيا أهل قرية استطعما أهلها فأبوا أن يضيفوهما فوجدا فيها جدارا يريد أن ينقض فأقامه قال لو شئت لاتخذت عليه أجرا |
| | | Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe. (Mũsã) ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa." |
|
2218 | 18 | 78 | قال هذا فراق بيني وبينك سأنبئك بتأويل ما لم تستطع عليه صبرا |
| | | Ya ce: "Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Zã ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa." |
|
2219 | 18 | 79 | أما السفينة فكانت لمساكين يعملون في البحر فأردت أن أعيبها وكان وراءهم ملك يأخذ كل سفينة غصبا |
| | | "Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce. |
|
2220 | 18 | 80 | وأما الغلام فكان أبواه مؤمنين فخشينا أن يرهقهما طغيانا وكفرا |
| | | "Kuma amma yaron, to, uwãyensa sun kasance mũminai, to, sai muka ji tsõron ya kallafa musu kangara da kãfirci." |
|
2221 | 18 | 81 | فأردنا أن يبدلهما ربهما خيرا منه زكاة وأقرب رحما |
| | | "Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alhẽri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi." |
|