نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2198 | 18 | 58 | وربك الغفور ذو الرحمة لو يؤاخذهم بما كسبوا لعجل لهم العذاب بل لهم موعد لن يجدوا من دونه موئلا |
| | | Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa. |
|
2199 | 18 | 59 | وتلك القرى أهلكناهم لما ظلموا وجعلنا لمهلكهم موعدا |
| | | Kuma waɗancan alƙaryu Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka su. |
|
2200 | 18 | 60 | وإذ قال موسى لفتاه لا أبرح حتى أبلغ مجمع البحرين أو أمضي حقبا |
| | | Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru." |
|
2201 | 18 | 61 | فلما بلغا مجمع بينهما نسيا حوتهما فاتخذ سبيله في البحر سربا |
| | | To, a lõkacin da suka isa mahaɗar tsakãninsu sai suka manta kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin tẽku kamar bĩga. |
|
2202 | 18 | 62 | فلما جاوزا قال لفتاه آتنا غداءنا لقد لقينا من سفرنا هذا نصبا |
| | | To, a lõkacin da suka wuce ya ce wa yãronsa, "Ka kãwo mana kãlãcinmu. Lalle ne haƙĩƙa mun haɗu da wahala daga tafiyarmu wannan." |
|
2203 | 18 | 63 | قال أرأيت إذ أوينا إلى الصخرة فإني نسيت الحوت وما أنسانيه إلا الشيطان أن أذكره واتخذ سبيله في البحر عجبا |
| | | (Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan, dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki!" |
|
2204 | 18 | 64 | قال ذلك ما كنا نبغ فارتدا على آثارهما قصصا |
| | | Ya ce: "Wancan ne abin da muka kasance munã biɗã." Sai suka kõma a kan gurãbunsu, sunã bĩbiya. |
|
2205 | 18 | 65 | فوجدا عبدا من عبادنا آتيناه رحمة من عندنا وعلمناه من لدنا علما |
| | | Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyinMu, Mun bã shi wata rahama daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gunMu. |
|
2206 | 18 | 66 | قال له موسى هل أتبعك على أن تعلمن مما علمت رشدا |
| | | Mũsã ya ce masa, "Ko in bĩ ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?" |
|
2207 | 18 | 67 | قال إنك لن تستطيع معي صبرا |
| | | Ya ce: "Lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ, ba." |
|