نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2144 | 18 | 4 | وينذر الذين قالوا اتخذ الله ولدا |
| | | Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce: "Allah yanã da ɗa." |
|
2145 | 18 | 5 | ما لهم به من علم ولا لآبائهم كبرت كلمة تخرج من أفواههم إن يقولون إلا كذبا |
| | | Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya. |
|
2146 | 18 | 6 | فلعلك باخع نفسك على آثارهم إن لم يؤمنوا بهذا الحديث أسفا |
| | | To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki. |
|
2147 | 18 | 7 | إنا جعلنا ما على الأرض زينة لها لنبلوهم أيهم أحسن عملا |
| | | Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki. |
|
2148 | 18 | 8 | وإنا لجاعلون ما عليها صعيدا جرزا |
| | | Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓãya ƙeƙasasshiya ne. |
|
2149 | 18 | 9 | أم حسبت أن أصحاب الكهف والرقيم كانوا من آياتنا عجبا |
| | | Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah? |
|
2150 | 18 | 10 | إذ أوى الفتية إلى الكهف فقالوا ربنا آتنا من لدنك رحمة وهيئ لنا من أمرنا رشدا |
| | | A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu." |
|
2151 | 18 | 11 | فضربنا على آذانهم في الكهف سنين عددا |
| | | Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu, a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa. |
|
2152 | 18 | 12 | ثم بعثناهم لنعلم أي الحزبين أحصى لما لبثوا أمدا |
| | | Sa'an nan Muka tãyar da su, dõmin Mu san wane ɗayan ƙungiyõyin biyu suka fi lissãfi ga abin da suka zauna na lõkacin. |
|
2153 | 18 | 13 | نحن نقص عليك نبأهم بالحق إنهم فتية آمنوا بربهم وزدناهم هدى |
| | | Mu ne ke jẽranta maka lãbãrinsu da gaskiya. Lalle ne sũ, waɗansu samãri ne. Sun yi ĩmãni da Ubangijinsu, kuma Muka ƙãra musu wata shiriya. |
|