نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2132 | 17 | 103 | فأراد أن يستفزهم من الأرض فأغرقناه ومن معه جميعا |
| | | Sai ya yi nufin fitar da su daga ƙasar, sai Muka nutsar da shi, shi da wanda yake tãre da shi gabã ɗaya. |
|
2133 | 17 | 104 | وقلنا من بعده لبني إسرائيل اسكنوا الأرض فإذا جاء وعد الآخرة جئنا بكم لفيفا |
| | | Kuma Muka ce: daga bãyansa ga Banĩ Isrã'ĩla, "Ku zauni ƙasar. Sa'an nan idan wa'adin ƙarshe ya zo, zã Mu jẽ da ku jama'a-jama'a." |
|
2134 | 17 | 105 | وبالحق أنزلناه وبالحق نزل وما أرسلناك إلا مبشرا ونذيرا |
| | | Kuma da gaskiya Muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Kuma ba Mu aike ka ba fãce kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. |
|
2135 | 17 | 106 | وقرآنا فرقناه لتقرأه على الناس على مكث ونزلناه تنزيلا |
| | | Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa. |
|
2136 | 17 | 107 | قل آمنوا به أو لا تؤمنوا إن الذين أوتوا العلم من قبله إذا يتلى عليهم يخرون للأذقان سجدا |
| | | Ka ce: "Ku yi ĩmãni da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada." |
|
2137 | 17 | 108 | ويقولون سبحان ربنا إن كان وعد ربنا لمفعولا |
| | | "Kuma sunã cẽwa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle ne wa'adin Ubangijinmu ya kasance, haƙĩƙa, abin aikatãwa." |
|
2138 | 17 | 109 | ويخرون للأذقان يبكون ويزيدهم خشوعا |
| | | Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu sunã kũka, kuma yanã ƙara musu tsõro. |
|
2139 | 17 | 110 | قل ادعوا الله أو ادعوا الرحمن أيا ما تدعوا فله الأسماء الحسنى ولا تجهر بصلاتك ولا تخافت بها وابتغ بين ذلك سبيلا |
| | | Ka ce: "Ku kirayi Allah kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan." |
|
2140 | 17 | 111 | وقل الحمد لله الذي لم يتخذ ولدا ولم يكن له شريك في الملك ولم يكن له ولي من الذل وكبره تكبيرا |
| | | Kuma ka ce: "Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba." Kuma ka girmama Shi, girmamãwa. |
|
2141 | 18 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله الذي أنزل على عبده الكتاب ولم يجعل له عوجا |
| | | Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi. |
|