نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2080 | 17 | 51 | أو خلقا مما يكبر في صدوركم فسيقولون من يعيدنا قل الذي فطركم أول مرة فسينغضون إليك رءوسهم ويقولون متى هو قل عسى أن يكون قريبا |
| | | "Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To zã su ce "Wãne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci." To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce: "Akwai tsammãninsa ya kasance kusa." |
|
2081 | 17 | 52 | يوم يدعوكم فتستجيبون بحمده وتظنون إن لبثتم إلا قليلا |
| | | "A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan." |
|
2082 | 17 | 53 | وقل لعبادي يقولوا التي هي أحسن إن الشيطان ينزغ بينهم إن الشيطان كان للإنسان عدوا مبينا |
| | | Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyananne. |
|
2083 | 17 | 54 | ربكم أعلم بكم إن يشأ يرحمكم أو إن يشأ يعذبكم وما أرسلناك عليهم وكيلا |
| | | Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba. |
|
2084 | 17 | 55 | وربك أعلم بمن في السماوات والأرض ولقد فضلنا بعض النبيين على بعض وآتينا داوود زبورا |
| | | Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra. |
|
2085 | 17 | 56 | قل ادعوا الذين زعمتم من دونه فلا يملكون كشف الضر عنكم ولا تحويلا |
| | | Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa." To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa." |
|
2086 | 17 | 57 | أولئك الذين يدعون يبتغون إلى ربهم الوسيلة أيهم أقرب ويرجون رحمته ويخافون عذابه إن عذاب ربك كان محذورا |
| | | Waɗancan, waɗanda suke kiran, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce. |
|
2087 | 17 | 58 | وإن من قرية إلا نحن مهلكوها قبل يوم القيامة أو معذبوها عذابا شديدا كان ذلك في الكتاب مسطورا |
| | | Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce. |
|
2088 | 17 | 59 | وما منعنا أن نرسل بالآيات إلا أن كذب بها الأولون وآتينا ثمود الناقة مبصرة فظلموا بها وما نرسل بالآيات إلا تخويفا |
| | | Kuma bãbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ãyõyi fãce sabõda mutãnen farko sun ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdãwa tãguwa, ãyã bayyananna, sai suka yi zãlunci game da ita. Kuma bã Mu aikãwa da ãyõyi fãce dõmin tsõratarwa. |
|
2089 | 17 | 60 | وإذ قلنا لك إن ربك أحاط بالناس وما جعلنا الرؤيا التي أريناك إلا فتنة للناس والشجرة الملعونة في القرآن ونخوفهم فما يزيدهم إلا طغيانا كبيرا |
| | | Kuma a lõkacin da Muka ce maka, "Lalle ne Ubangijinka Yã kẽwaye mutãne." Kuma ba Mu sanya abin da ya gani wanda Muka nũna maka ba, fãce dõmin fitina ga mutãne, da itãciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Munã tsõratar da su, sa'an nan (tsõratarwar) bã ta ƙãra su fãce da kangara mai girma. |
|