نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2045 | 17 | 16 | وإذا أردنا أن نهلك قرية أمرنا مترفيها ففسقوا فيها فحق عليها القول فدمرناها تدميرا |
| | | Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fãsicci a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa. |
|
2046 | 17 | 17 | وكم أهلكنا من القرون من بعد نوح وكفى بربك بذنوب عباده خبيرا بصيرا |
| | | Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani. |
|
2047 | 17 | 18 | من كان يريد العاجلة عجلنا له فيها ما نشاء لمن نريد ثم جعلنا له جهنم يصلاها مذموما مدحورا |
| | | Wanda ya kasance yanã nufin mai gaggãwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙõnu da ita, yanã abin zargi kuma abin tunkuɗewa. |
|
2048 | 17 | 19 | ومن أراد الآخرة وسعى لها سعيها وهو مؤمن فأولئك كان سعيهم مشكورا |
| | | Kuma wanda ya nufi Lãhira, kuma ya yi aiki sabõda ita irin aikinta alhãli kuwa yanã mũmĩni, to, waɗannan aikinsu ya kasance gõdadde. |
|
2049 | 17 | 20 | كلا نمد هؤلاء وهؤلاء من عطاء ربك وما كان عطاء ربك محظورا |
| | | Dukkansu Munã taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba. |
|
2050 | 17 | 21 | انظر كيف فضلنا بعضهم على بعض وللآخرة أكبر درجات وأكبر تفضيلا |
| | | Ka duba yadda Muka fĩfĩtar da sãshensu a kan sãshe! Kuma lalle ne Lãhira ce mafi girman darajõji, kuma mafi girman fĩfĩtãwa. |
|
2051 | 17 | 22 | لا تجعل مع الله إلها آخر فتقعد مذموما مخذولا |
| | | Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tãre da Allah har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe. |
|
2052 | 17 | 23 | وقضى ربك ألا تعبدوا إلا إياه وبالوالدين إحسانا إما يبلغن عندك الكبر أحدهما أو كلاهما فلا تقل لهما أف ولا تنهرهما وقل لهما قولا كريما |
| | | Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci. |
|
2053 | 17 | 24 | واخفض لهما جناح الذل من الرحمة وقل رب ارحمهما كما ربياني صغيرا |
| | | Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami." |
|
2054 | 17 | 25 | ربكم أعلم بما في نفوسكم إن تكونوا صالحين فإنه كان للأوابين غفورا |
| | | Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rãyukanku. Idan kun kasance sãlihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga mãsu kõmawa gare Shi, Mai gãfara. |
|