نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2036 | 17 | 7 | إن أحسنتم أحسنتم لأنفسكم وإن أسأتم فلها فإذا جاء وعد الآخرة ليسوءوا وجوهكم وليدخلوا المسجد كما دخلوه أول مرة وليتبروا ما علوا تتبيرا |
| | | Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe ya jẽ, (za su je) dõmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa. |
|
2037 | 17 | 8 | عسى ربكم أن يرحمكم وإن عدتم عدنا وجعلنا جهنم للكافرين حصيرا |
| | | Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai. |
|
2038 | 17 | 9 | إن هذا القرآن يهدي للتي هي أقوم ويبشر المؤمنين الذين يعملون الصالحات أن لهم أجرا كبيرا |
| | | Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma." |
|
2039 | 17 | 10 | وأن الذين لا يؤمنون بالآخرة أعتدنا لهم عذابا أليما |
| | | Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. |
|
2040 | 17 | 11 | ويدع الإنسان بالشر دعاءه بالخير وكان الإنسان عجولا |
| | | Kuma mutum yanã yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa. |
|
2041 | 17 | 12 | وجعلنا الليل والنهار آيتين فمحونا آية الليل وجعلنا آية النهار مبصرة لتبتغوا فضلا من ربكم ولتعلموا عدد السنين والحساب وكل شيء فصلناه تفصيلا |
| | | Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanãwa. |
|
2042 | 17 | 13 | وكل إنسان ألزمناه طائره في عنقه ونخرج له يوم القيامة كتابا يلقاه منشورا |
| | | Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar ¡iyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe. |
|
2043 | 17 | 14 | اقرأ كتابك كفى بنفسك اليوم عليك حسيبا |
| | | "Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau." |
|
2044 | 17 | 15 | من اهتدى فإنما يهتدي لنفسه ومن ضل فإنما يضل عليها ولا تزر وازرة وزر أخرى وما كنا معذبين حتى نبعث رسولا |
| | | Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo. |
|
2045 | 17 | 16 | وإذا أردنا أن نهلك قرية أمرنا مترفيها ففسقوا فيها فحق عليها القول فدمرناها تدميرا |
| | | Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fãsicci a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa. |
|