نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2014 | 16 | 113 | ولقد جاءهم رسول منهم فكذبوه فأخذهم العذاب وهم ظالمون |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci. |
|
2015 | 16 | 114 | فكلوا مما رزقكم الله حلالا طيبا واشكروا نعمت الله إن كنتم إياه تعبدون |
| | | Sa'an nan ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa. |
|
2016 | 16 | 115 | إنما حرم عليكم الميتة والدم ولحم الخنزير وما أهل لغير الله به فمن اضطر غير باغ ولا عاد فإن الله غفور رحيم |
| | | Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. |
|
2017 | 16 | 116 | ولا تقولوا لما تصف ألسنتكم الكذب هذا حلال وهذا حرام لتفتروا على الله الكذب إن الذين يفترون على الله الكذب لا يفلحون |
| | | Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba. |
|
2018 | 16 | 117 | متاع قليل ولهم عذاب أليم |
| | | Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi. |
|
2019 | 16 | 118 | وعلى الذين هادوا حرمنا ما قصصنا عليك من قبل وما ظلمناهم ولكن كانوا أنفسهم يظلمون |
| | | Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta. |
|
2020 | 16 | 119 | ثم إن ربك للذين عملوا السوء بجهالة ثم تابوا من بعد ذلك وأصلحوا إن ربك من بعدها لغفور رحيم |
| | | Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
|
2021 | 16 | 120 | إن إبراهيم كان أمة قانتا لله حنيفا ولم يك من المشركين |
| | | Lalle ne Ibrãhĩm ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba. |
|
2022 | 16 | 121 | شاكرا لأنعمه اجتباه وهداه إلى صراط مستقيم |
| | | Mai gõdiya ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici. |
|
2023 | 16 | 122 | وآتيناه في الدنيا حسنة وإنه في الآخرة لمن الصالحين |
| | | Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai. |
|