نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1982 | 16 | 81 | والله جعل لكم مما خلق ظلالا وجعل لكم من الجبال أكنانا وجعل لكم سرابيل تقيكم الحر وسرابيل تقيكم بأسكم كذلك يتم نعمته عليكم لعلكم تسلمون |
| | | Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa. |
|
1983 | 16 | 82 | فإن تولوا فإنما عليك البلاغ المبين |
| | | To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã. |
|
1984 | 16 | 83 | يعرفون نعمت الله ثم ينكرونها وأكثرهم الكافرون |
| | | Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne. |
|
1985 | 16 | 84 | ويوم نبعث من كل أمة شهيدا ثم لا يؤذن للذين كفروا ولا هم يستعتبون |
| | | Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba. |
|
1986 | 16 | 85 | وإذا رأى الذين ظلموا العذاب فلا يخفف عنهم ولا هم ينظرون |
| | | Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba. |
|
1987 | 16 | 86 | وإذا رأى الذين أشركوا شركاءهم قالوا ربنا هؤلاء شركاؤنا الذين كنا ندعو من دونك فألقوا إليهم القول إنكم لكاذبون |
| | | Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne." |
|
1988 | 16 | 87 | وألقوا إلى الله يومئذ السلم وضل عنهم ما كانوا يفترون |
| | | Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su. |
|
1989 | 16 | 88 | الذين كفروا وصدوا عن سبيل الله زدناهم عذابا فوق العذاب بما كانوا يفسدون |
| | | Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi. |
|
1990 | 16 | 89 | ويوم نبعث في كل أمة شهيدا عليهم من أنفسهم وجئنا بك شهيدا على هؤلاء ونزلنا عليك الكتاب تبيانا لكل شيء وهدى ورحمة وبشرى للمسلمين |
| | | Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi). |
|
1991 | 16 | 90 | إن الله يأمر بالعدل والإحسان وإيتاء ذي القربى وينهى عن الفحشاء والمنكر والبغي يعظكم لعلكم تذكرون |
| | | Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa. |
|