نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1884 | 15 | 82 | وكانوا ينحتون من الجبال بيوتا آمنين |
| | | Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu. |
|
1885 | 15 | 83 | فأخذتهم الصيحة مصبحين |
| | | Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba. |
|
1886 | 15 | 84 | فما أغنى عنهم ما كانوا يكسبون |
| | | Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba. |
|
1887 | 15 | 85 | وما خلقنا السماوات والأرض وما بينهما إلا بالحق وإن الساعة لآتية فاصفح الصفح الجميل |
| | | Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau. |
|
1888 | 15 | 86 | إن ربك هو الخلاق العليم |
| | | Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani. |
|
1889 | 15 | 87 | ولقد آتيناك سبعا من المثاني والقرآن العظيم |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma. |
|
1890 | 15 | 88 | لا تمدن عينيك إلى ما متعنا به أزواجا منهم ولا تحزن عليهم واخفض جناحك للمؤمنين |
| | | Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni. |
|
1891 | 15 | 89 | وقل إني أنا النذير المبين |
| | | Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne." |
|
1892 | 15 | 90 | كما أنزلنا على المقتسمين |
| | | Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa, |
|
1893 | 15 | 91 | الذين جعلوا القرآن عضين |
| | | Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi. |
|