نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1879 | 15 | 77 | إن في ذلك لآية للمؤمنين |
| | | Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni. |
|
1880 | 15 | 78 | وإن كان أصحاب الأيكة لظالمين |
| | | Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci! |
|
1881 | 15 | 79 | فانتقمنا منهم وإنهما لبإمام مبين |
| | | Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani. |
|
1882 | 15 | 80 | ولقد كذب أصحاب الحجر المرسلين |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni. |
|
1883 | 15 | 81 | وآتيناهم آياتنا فكانوا عنها معرضين |
| | | Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su. |
|
1884 | 15 | 82 | وكانوا ينحتون من الجبال بيوتا آمنين |
| | | Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu. |
|
1885 | 15 | 83 | فأخذتهم الصيحة مصبحين |
| | | Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba. |
|
1886 | 15 | 84 | فما أغنى عنهم ما كانوا يكسبون |
| | | Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba. |
|
1887 | 15 | 85 | وما خلقنا السماوات والأرض وما بينهما إلا بالحق وإن الساعة لآتية فاصفح الصفح الجميل |
| | | Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau. |
|
1888 | 15 | 86 | إن ربك هو الخلاق العليم |
| | | Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani. |
|