نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1870 | 15 | 68 | قال إن هؤلاء ضيفي فلا تفضحون |
| | | Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni." |
|
1871 | 15 | 69 | واتقوا الله ولا تخزون |
| | | "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki." |
|
1872 | 15 | 70 | قالوا أولم ننهك عن العالمين |
| | | Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?" |
|
1873 | 15 | 71 | قال هؤلاء بناتي إن كنتم فاعلين |
| | | Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne." |
|
1874 | 15 | 72 | لعمرك إنهم لفي سكرتهم يعمهون |
| | | Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa. |
|
1875 | 15 | 73 | فأخذتهم الصيحة مشرقين |
| | | Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã. |
|
1876 | 15 | 74 | فجعلنا عاليها سافلها وأمطرنا عليهم حجارة من سجيل |
| | | Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu. |
|
1877 | 15 | 75 | إن في ذلك لآيات للمتوسمين |
| | | Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali. |
|
1878 | 15 | 76 | وإنها لبسبيل مقيم |
| | | Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya. |
|
1879 | 15 | 77 | إن في ذلك لآية للمؤمنين |
| | | Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni. |
|