نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1862 | 15 | 60 | إلا امرأته قدرنا إنها لمن الغابرين |
| | | "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka." |
|
1863 | 15 | 61 | فلما جاء آل لوط المرسلون |
| | | To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu, |
|
1864 | 15 | 62 | قال إنكم قوم منكرون |
| | | Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba." |
|
1865 | 15 | 63 | قالوا بل جئناك بما كانوا فيه يمترون |
| | | Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa." |
|
1866 | 15 | 64 | وأتيناك بالحق وإنا لصادقون |
| | | "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne." |
|
1867 | 15 | 65 | فأسر بأهلك بقطع من الليل واتبع أدبارهم ولا يلتفت منكم أحد وامضوا حيث تؤمرون |
| | | "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku." |
|
1868 | 15 | 66 | وقضينا إليه ذلك الأمر أن دابر هؤلاء مقطوع مصبحين |
| | | Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba. |
|
1869 | 15 | 67 | وجاء أهل المدينة يستبشرون |
| | | Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra. |
|
1870 | 15 | 68 | قال إن هؤلاء ضيفي فلا تفضحون |
| | | Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni." |
|
1871 | 15 | 69 | واتقوا الله ولا تخزون |
| | | "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki." |
|