نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1836 | 15 | 34 | قال فاخرج منها فإنك رجيم |
| | | Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne." |
|
1837 | 15 | 35 | وإن عليك اللعنة إلى يوم الدين |
| | | "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako." |
|
1838 | 15 | 36 | قال رب فأنظرني إلى يوم يبعثون |
| | | Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su." |
|
1839 | 15 | 37 | قال فإنك من المنظرين |
| | | Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri." |
|
1840 | 15 | 38 | إلى يوم الوقت المعلوم |
| | | "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne." |
|
1841 | 15 | 39 | قال رب بما أغويتني لأزينن لهم في الأرض ولأغوينهم أجمعين |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya." |
|
1842 | 15 | 40 | إلا عبادك منهم المخلصين |
| | | "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake." |
|
1843 | 15 | 41 | قال هذا صراط علي مستقيم |
| | | Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici." |
|
1844 | 15 | 42 | إن عبادي ليس لك عليهم سلطان إلا من اتبعك من الغاوين |
| | | "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu." |
|
1845 | 15 | 43 | وإن جهنم لموعدهم أجمعين |
| | | Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya. |
|