نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1798 | 14 | 48 | يوم تبدل الأرض غير الأرض والسماوات وبرزوا لله الواحد القهار |
| | | A rãnar da ake musanya ƙasa bã ƙasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makaɗaici, Mai tanƙwasãwa. |
|
1799 | 14 | 49 | وترى المجرمين يومئذ مقرنين في الأصفاد |
| | | Kuma kana ganin mãsu laifi, a rãnar nan, sunã waɗanda aka yi wa ciri daidai a cikin marũruwa. |
|
1800 | 14 | 50 | سرابيلهم من قطران وتغشى وجوههم النار |
| | | Rigunansu daga farar wutã ne, kuma wuta ta rufe fuskõkinsu. |
|
1801 | 14 | 51 | ليجزي الله كل نفس ما كسبت إن الله سريع الحساب |
| | | Dõmin Allah Ya sãkã wa kõwane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah Mai gaggãwar hisãbi ne. |
|
1802 | 14 | 52 | هذا بلاغ للناس ولينذروا به وليعلموا أنما هو إله واحد وليذكر أولو الألباب |
| | | Wannan iyarwa ce ga mutãne, kuma dõmin a yi musu gargaɗi da shi, kuma dõmin su sani cẽwa, abin sani kawai, shĩ ne abin bautawa guda. Kuma dõmin masu hankali su riƙa tunãwa. |
|
1803 | 15 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الر تلك آيات الكتاب وقرآن مبين |
| | | A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa. |
|
1804 | 15 | 2 | ربما يود الذين كفروا لو كانوا مسلمين |
| | | Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi. |
|
1805 | 15 | 3 | ذرهم يأكلوا ويتمتعوا ويلههم الأمل فسوف يعلمون |
| | | Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani. |
|
1806 | 15 | 4 | وما أهلكنا من قرية إلا ولها كتاب معلوم |
| | | Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne. |
|
1807 | 15 | 5 | ما تسبق من أمة أجلها وما يستأخرون |
| | | Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba. |
|