نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1739 | 13 | 32 | ولقد استهزئ برسل من قبلك فأمليت للذين كفروا ثم أخذتهم فكيف كان عقاب |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da Manzanni kãfinka, sai Na yi jinkiri ga waɗanda suka kãfirta, sa'an nan Na kãma su. To, yãya uƙũbãta take? |
|
1740 | 13 | 33 | أفمن هو قائم على كل نفس بما كسبت وجعلوا لله شركاء قل سموهم أم تنبئونه بما لا يعلم في الأرض أم بظاهر من القول بل زين للذين كفروا مكرهم وصدوا عن السبيل ومن يضلل الله فما له من هاد |
| | | Shin fa, wanda shĩ Yake tsaye a kan kõwane rai game da abin da ya tanada (zai zama kamar wanda ba haka ba)? Kuma suka sanya abõkan tãrayya ga Allah! Ka ce: "Ku ambaci sũnãyensu."Ko kunã bai wa Allah lãbãri ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Kõ da bayyananniyar magana kuke yin shirka, (banda a cikin zũciya)? Ã'a, an dai ƙawãta wa waɗanda suka kafirta mãkircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bãbu wani mai shiryarwa a gare shi!" |
|
1741 | 13 | 34 | لهم عذاب في الحياة الدنيا ولعذاب الآخرة أشق وما لهم من الله من واق |
| | | Sunã da wata azãba a cikin rãyuwar dũniya, kuma haƙĩƙa azãbar Lãhira ce mafi tsanani kuma bãbu wani mai tsare su daga Allah. |
|
1742 | 13 | 35 | مثل الجنة التي وعد المتقون تجري من تحتها الأنهار أكلها دائم وظلها تلك عقبى الذين اتقوا وعقبى الكافرين النار |
| | | Misãlin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga mãsu taƙawa, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma ãƙibar kãfirai, ita ce wuta, |
|
1743 | 13 | 36 | والذين آتيناهم الكتاب يفرحون بما أنزل إليك ومن الأحزاب من ينكر بعضه قل إنما أمرت أن أعبد الله ولا أشرك به إليه أدعو وإليه مآب |
| | | Kuma waɗanda Muka bã su Littãfi sunã farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyõyi akwai mai musun sãshensa. Ka ce: "Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makõmata take." |
|
1744 | 13 | 37 | وكذلك أنزلناه حكما عربيا ولئن اتبعت أهواءهم بعدما جاءك من العلم ما لك من الله من ولي ولا واق |
| | | Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi, Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari. |
|
1745 | 13 | 38 | ولقد أرسلنا رسلا من قبلك وجعلنا لهم أزواجا وذرية وما كان لرسول أن يأتي بآية إلا بإذن الله لكل أجل كتاب |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali akwai littãfi. |
|
1746 | 13 | 39 | يمحو الله ما يشاء ويثبت وعنده أم الكتاب |
| | | Allah Yanã shafe abin da Yake so, kuma Yanã tabbatarwa kuma a wurinsa asalin Littãfin yake. |
|
1747 | 13 | 40 | وإن ما نرينك بعض الذي نعدهم أو نتوفينك فإنما عليك البلاغ وعلينا الحساب |
| | | Kuma imma lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu wa'adi, kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisãbi yana gare Mu. |
|
1748 | 13 | 41 | أولم يروا أنا نأتي الأرض ننقصها من أطرافها والله يحكم لا معقب لحكمه وهو سريع الحساب |
| | | Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako. |
|