نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1687 | 12 | 91 | قالوا تالله لقد آثرك الله علينا وإن كنا لخاطئين |
| | | Suka ce: "Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure." |
|
1688 | 12 | 92 | قال لا تثريب عليكم اليوم يغفر الله لكم وهو أرحم الراحمين |
| | | Ya ce: "Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama." |
|
1689 | 12 | 93 | اذهبوا بقميصي هذا فألقوه على وجه أبي يأت بصيرا وأتوني بأهلكم أجمعين |
| | | "Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya." |
|
1690 | 12 | 94 | ولما فصلت العير قال أبوهم إني لأجد ريح يوسف لولا أن تفندون |
| | | Kuma, a lõkacin da ãyari ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba." |
|
1691 | 12 | 95 | قالوا تالله إنك لفي ضلالك القديم |
| | | Suka ce: "Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa." |
|
1692 | 12 | 96 | فلما أن جاء البشير ألقاه على وجهه فارتد بصيرا قال ألم أقل لكم إني أعلم من الله ما لا تعلمون |
| | | Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?" |
|
1693 | 12 | 97 | قالوا يا أبانا استغفر لنا ذنوبنا إنا كنا خاطئين |
| | | Suka ce: "Yã ubanmu! ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure." |
|
1694 | 12 | 98 | قال سوف أستغفر لكم ربي إنه هو الغفور الرحيم |
| | | Ya ce: "Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." |
|
1695 | 12 | 99 | فلما دخلوا على يوسف آوى إليه أبويه وقال ادخلوا مصر إن شاء الله آمنين |
| | | Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu." |
|
1696 | 12 | 100 | ورفع أبويه على العرش وخروا له سجدا وقال يا أبت هذا تأويل رؤياي من قبل قد جعلها ربي حقا وقد أحسن بي إذ أخرجني من السجن وجاء بكم من البدو من بعد أن نزغ الشيطان بيني وبين إخوتي إن ربي لطيف لما يشاء إنه هو العليم الحكيم |
| | | Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada. Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, Shĩ ne Masani, Mai hikima." |
|