نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1685 | 12 | 89 | قال هل علمتم ما فعلتم بيوسف وأخيه إذ أنتم جاهلون |
| | | Ya ce: "Shin, kan san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?" |
|
1686 | 12 | 90 | قالوا أإنك لأنت يوسف قال أنا يوسف وهذا أخي قد من الله علينا إنه من يتق ويصبر فإن الله لا يضيع أجر المحسنين |
| | | Saka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa." |
|
1687 | 12 | 91 | قالوا تالله لقد آثرك الله علينا وإن كنا لخاطئين |
| | | Suka ce: "Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure." |
|
1688 | 12 | 92 | قال لا تثريب عليكم اليوم يغفر الله لكم وهو أرحم الراحمين |
| | | Ya ce: "Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama." |
|
1689 | 12 | 93 | اذهبوا بقميصي هذا فألقوه على وجه أبي يأت بصيرا وأتوني بأهلكم أجمعين |
| | | "Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya." |
|
1690 | 12 | 94 | ولما فصلت العير قال أبوهم إني لأجد ريح يوسف لولا أن تفندون |
| | | Kuma, a lõkacin da ãyari ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba." |
|
1691 | 12 | 95 | قالوا تالله إنك لفي ضلالك القديم |
| | | Suka ce: "Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa." |
|
1692 | 12 | 96 | فلما أن جاء البشير ألقاه على وجهه فارتد بصيرا قال ألم أقل لكم إني أعلم من الله ما لا تعلمون |
| | | Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?" |
|
1693 | 12 | 97 | قالوا يا أبانا استغفر لنا ذنوبنا إنا كنا خاطئين |
| | | Suka ce: "Yã ubanmu! ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure." |
|
1694 | 12 | 98 | قال سوف أستغفر لكم ربي إنه هو الغفور الرحيم |
| | | Ya ce: "Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." |
|