نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1668 | 12 | 72 | قالوا نفقد صواع الملك ولمن جاء به حمل بعير وأنا به زعيم |
| | | Suka ce: "Munã nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi." |
|
1669 | 12 | 73 | قالوا تالله لقد علمتم ما جئنا لنفسد في الأرض وما كنا سارقين |
| | | Suka ce: "Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba." |
|
1670 | 12 | 74 | قالوا فما جزاؤه إن كنتم كاذبين |
| | | Suka ce: "To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?" |
|
1671 | 12 | 75 | قالوا جزاؤه من وجد في رحله فهو جزاؤه كذلك نجزي الظالمين |
| | | Suka ce: "Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai." |
|
1672 | 12 | 76 | فبدأ بأوعيتهم قبل وعاء أخيه ثم استخرجها من وعاء أخيه كذلك كدنا ليوسف ما كان ليأخذ أخاه في دين الملك إلا أن يشاء الله نرفع درجات من نشاء وفوق كل ذي علم عليم |
| | | To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani. |
|
1673 | 12 | 77 | قالوا إن يسرق فقد سرق أخ له من قبل فأسرها يوسف في نفسه ولم يبدها لهم قال أنتم شر مكانا والله أعلم بما تصفون |
| | | Suka ce: "Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa." |
|
1674 | 12 | 78 | قالوا يا أيها العزيز إن له أبا شيخا كبيرا فخذ أحدنا مكانه إنا نراك من المحسنين |
| | | Suka ce: "Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa. Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa." |
|
1675 | 12 | 79 | قال معاذ الله أن نأخذ إلا من وجدنا متاعنا عنده إنا إذا لظالمون |
| | | Ya ce: "Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan, haƙĩƙa, azzãlumai ne." |
|
1676 | 12 | 80 | فلما استيأسوا منه خلصوا نجيا قال كبيرهم ألم تعلموا أن أباكم قد أخذ عليكم موثقا من الله ومن قبل ما فرطتم في يوسف فلن أبرح الأرض حتى يأذن لي أبي أو يحكم الله لي وهو خير الحاكمين |
| | | Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta." |
|
1677 | 12 | 81 | ارجعوا إلى أبيكم فقولوا يا أبانا إن ابنك سرق وما شهدنا إلا بما علمنا وما كنا للغيب حافظين |
| | | "Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba." |
|