نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1619 | 12 | 23 | وراودته التي هو في بيتها عن نفسه وغلقت الأبواب وقالت هيت لك قال معاذ الله إنه ربي أحسن مثواي إنه لا يفلح الظالمون |
| | | Kuma wadda yake a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!" |
|
1620 | 12 | 24 | ولقد همت به وهم بها لولا أن رأى برهان ربه كذلك لنصرف عنه السوء والفحشاء إنه من عبادنا المخلصين |
| | | Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake. |
|
1621 | 12 | 25 | واستبقا الباب وقدت قميصه من دبر وألفيا سيدها لدى الباب قالت ما جزاء من أراد بأهلك سوءا إلا أن يسجن أو عذاب أليم |
| | | Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi." |
|
1622 | 12 | 26 | قال هي راودتني عن نفسي وشهد شاهد من أهلها إن كان قميصه قد من قبل فصدقت وهو من الكاذبين |
| | | Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: "Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata." |
|
1623 | 12 | 27 | وإن كان قميصه قد من دبر فكذبت وهو من الصادقين |
| | | "Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya." |
|
1624 | 12 | 28 | فلما رأى قميصه قد من دبر قال إنه من كيدكن إن كيدكن عظيم |
| | | Sa'an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: "Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!" |
|
1625 | 12 | 29 | يوسف أعرض عن هذا واستغفري لذنبك إنك كنت من الخاطئين |
| | | "Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure." |
|
1626 | 12 | 30 | وقال نسوة في المدينة امرأت العزيز تراود فتاها عن نفسه قد شغفها حبا إنا لنراها في ضلال مبين |
| | | Kuma waɗansu mãtã a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna." |
|
1627 | 12 | 31 | فلما سمعت بمكرهن أرسلت إليهن وأعتدت لهن متكأ وآتت كل واحدة منهن سكينا وقالت اخرج عليهن فلما رأينه أكبرنه وقطعن أيديهن وقلن حاش لله ما هذا بشرا إن هذا إلا ملك كريم |
| | | Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!" |
|
1628 | 12 | 32 | قالت فذلكن الذي لمتنني فيه ولقد راودته عن نفسه فاستعصم ولئن لم يفعل ما آمره ليسجنن وليكونا من الصاغرين |
| | | Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu." |
|